Nigerian news All categories All tags
Gwamna Yahaya Bello ya shiga tsaka mai wuya, hukumar INEC ta ce su hadu a kotu

Gwamna Yahaya Bello ya shiga tsaka mai wuya, hukumar INEC ta ce su hadu a kotu

- Hukumar zabe (INEC) ta ce har yanzu tana kan bakan ta na maka gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a kotu

- Kotun zata shiga da karar gwamnan bisa laifin yin rijistar zabe guda biyu

- Yahaya Bello ya yi rijistar katin zabe guda biyu, daya a Abuja, daya kuma a jihar Kogi

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa (INEC) ta ce har yanzu tana nan kan batun ta na maka gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a kotu bisa laifin yin rijistar zabe guda biyu.

Kwamishinan INEC a jihar Kogi, James Apam, ne ya bayyana hakan a Lokoja, babban birnin jihar ranar Alhamis.

"Bamu yi shakulatin bangaro da batun laifin rijistar zabe guda biyu da gwamna Bello ya yi ba. Ba zamu iya gurfanar da shi yanzu ba saboda yana da kariyar mulki," inji Apam.

Gwamna Yahaya Bello ya shiga tsaka mai wuya, hukumar INEC ta ce su hadu a kotu

Gwamna Yahaya Bello

Ya kara da cewa "ya aikata laifi kuma dole a yi masa hukunci."

Apam ya ce bayar da katin zabe na wucin gadi ga gwamnan ba yana nufin hukumar INEC ba zata dauki mataki a kansa ba ne.

A ranar 26 ga watan Fabrairu hukumar INEC ta bayar da katin zabe na wucin gadi ga gwamna Bello bayan ya cike takardar neman canjin wurin kada kuri'a daga Abuja zuwa Okene.

KARANTA WANNAN: Tsawon shekaru 20 Najeriya bata samu sukuni ba sai yanzu - Buhari

Hukumar INEC na tuhumar Bello da yin rijistar zabe guda biyu; daya a Abuja kafin ya zama gwamna, daya kuma a gidan gwamnatin jihar Kogi bayan ya zama gwamna.

Hukumar zabe ta bakin daya daga cikin kwamishinonin ta na kasa, Emmanuel Shoyebi, ta ce yin rijistar zabe laifi ne da ya saba da kundin dokokin hukumar INEC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel