Nigerian news All categories All tags
Layin mai: Hukumar NNPC ta bayyana adadin yawan man da ta shigo da shi kawo yanzu

Layin mai: Hukumar NNPC ta bayyana adadin yawan man da ta shigo da shi kawo yanzu

Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari a ta hannun kamfanin dake kula da albarkatun man fetur ya bayyana cewa kawo yanzu ya shigo da fetur da ya kai na $5.8 biliyan.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban ta Dakta Mai Kanti Baru yayin da yake ansa tambayoyi a gaban kwamitin majalisar dattijai dake sa ido game da harkokin hukumar.

Layin mai: Hukumar NNPC ta bayyana adadin yawan man da ta shigo da shi kawo yanzu

Layin mai: Hukumar NNPC ta bayyana adadin yawan man da ta shigo da shi kawo yanzu

KU KARANTA: Kotu ta ba da belin Sanata Dino Melaye Naira dubu 10

Legit.ng ta samu dai cewa shugaban hukumar, wanda babban jami'in hukumar da ke kula da harkokin kudi Abdulrazaq Isiaka ya bayyana cewa sun shigo da su ne domin saukakawa 'yan kasar wahalar da suke sha wajen samun man.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyara Najeriya a karkashi jagorancin shugaba Muhammadu Buhari tayi wa ma'aikatan ta albishir mai dadin gaske game da karin albashin da za ta yi masu zuwa nan da karshen watan Satumba mai zuwa.

Sakataren gwamnatin tarayyar ne dai Mista Boss Mustapha ya bayyana cewa karin albashin da gwamnatin zata yi zai yi dai dai da tadda tattalin arzikin Najeriya din yake kuma gwamnatin za ta yi adalci wajen dabbaka shirin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel