Nigerian news All categories All tags
Tsawon shekaru 20 Najeriya bata samu sukuni ba sai yanzu - Buhari

Tsawon shekaru 20 Najeriya bata samu sukuni ba sai yanzu - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sai yanzu Najeriya ta fita daga kangin tattalin arziki na tsawon shekaru 20

- Buhari ya furta wannan kalami ne yayin karbar bakuncin jakadan kasar Qatar a fadar sa

- Ya ce samun karuwar masu zuba jari a Najeriya alama ce ta samun nasarar gwamnatin sa a bangaren farfado da tattalin arziki

A yammacin yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar sai yanzu Najeriya ta fita daga kangin matsin tattalin arziki da ya shake mata wuya na tsawon shekaru 20.

A cewar Buhari, samun karuwar masu zuba jari a cikin Najeriya alama ce dake nuna samun nasarar gwamnatin sa a bangaren farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Shugaba Buhari na furta wadannan kalamai ne yayin karbar bakuncin wasu 'yan kasuwa daga kasar Qatar karkashin jagorancin tsohon sarkin kasar, Sheikh Hamad Bin Khalifa Al-Thani a fadar gwamnatin tarayya.

Tsawon shekaru 20 Najeriya bata samu sukuni ba sai yanzu - Buhari

shugaba Buhari da Sheikh Al-Thani

Shugaba Buhari ya bayyana cewar manufar tsarin sa na tattalin arziki shine dora Najeriya a kan hanyar noma tare da rage dogaro a kan man fetur.

KARANTA WANNAN: Karin wa'adin shugabannin jam'iyya: APC ta haka kabarin binne kan ta - PDP

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya taba furta cewar zuwan shugaba Buhari ya saka Najeriya cikin jerin kasashe da ake tururuwar zuwa domin saka jari.

A nasa jawabin, Sheikh Al-Thani, ya ce shugaba Buhari ya bunkasa kimar Najeriya a idanun masu son zuwa kasar domin yin kasuwanci ta hanyar yaki da cin hanci da kuma girmama doka da oda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel