Nigerian news All categories All tags
Karin albashi: Gwamnatin tarayya ta ayyana muhimmin albishir ga ma'aikata

Karin albashi: Gwamnatin tarayya ta ayyana muhimmin albishir ga ma'aikata

Gwamnatin tarayyara Najeriya a karkashi jagorancin shugaba Muhammadu Buhari tayi wa ma'aikatan ta albishir mai dadin gaske game da karin albashin da za ta yi masu zuwa nan da karshen watan Satumba mai zuwa.

Sakataren gwamnatin tarayyar ne dai Mista Boss Mustapha ya bayyana cewa karin albashin da gwamnatin zata yi zai yi dai dai da tadda tattalin arzikin Najeriya din yake kuma gwamnatin za ta yi adalci wajen dabbaka shirin.

Karin albashi: Gwamnatin tarayya ta ayyana muhimmin albishir ga ma'aikata

Karin albashi: Gwamnatin tarayya ta ayyana muhimmin albishir ga ma'aikata

KU KARANTA: An gano gidajen alfarma 2 na Sanata Ekweremadu a Landan

Legit.ng dai ta samu cewa Mista Boss Mustapha yayi wannan bayanan ne a yayin wata walimar cin abincin dare da kungiyar kwadago ta kasa watau NLC ta shirya domin bikin cikar ta shekaru 40 da kafuwa da kuma ta gudana a garin Abuja.

A wani labarin kuma, Majalisar wakilan Najeriya a yau sun yi tofin Allah-tsine tare da nuna rashin gamsuwa da salon mulki na ministocin gwamnatin shugaba Buhari dake da alhakin kula da ma'adinai da karafa watau Mista Kayode Fayemi da kuma mataimakin sa Abubakar Bwari.

'Yan majalisun dai a yayin zaman na su na yau sun kuma yi kakkausan furuci ga ministocin bisa ga kin mutunta kiran da suka yi masu suyi masu bayani kan yadda harkar kamfanin karafa na Ajaokuta yake.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel