Nigerian news All categories All tags
Gwamnonin arewa fara gudanar da wani muhimmin taro a garin Kaduna

Gwamnonin arewa fara gudanar da wani muhimmin taro a garin Kaduna

A yau din nan ne dai dukkanin gwamnonin arewacin Najeriya suka hallara a garin Kaduna babban birnin jihar ta Kaduna domin fara wani muhimmin taro da zai yi duban tsanaki ga matsalolin da suka addabin yankin da suka hada da matsalar tsaro da kuma sauya fasalin kasa.

Shugaban gwamnonin na Arewa wanda kuma ke zaman Gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shetima a lokacin bude taron ya bayyana cewa a matsayin su na gwamnoni kuma wakilan al'umma sun ga cewar ya kamata su hadu wuri guda domin tattauna makomar yankin da kuma mutanen dake rayuwa a cikin sa.

Gwamnonin arewa fara gudanar da wani muhimmin taro a garin Kaduna

Gwamnonin arewa fara gudanar da wani muhimmin taro a garin Kaduna

KU KARANTA: Majalisar wakilai sun yi tofin Alla-tsine ga ministocin Buhari 2

Legit.ng ta samu cewa gwamnan ya kuma kara da cewa daga karshen taron za su fitar da sanarwa da zata bayyana dukkan matsayar da suka dauka wanda a cewar sa kuma hakan ba zai ci karo da irin matakan da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke dauka ba.

A wani labarin kuma, Labarin da muka samu maras dadi daga majiyar mu ta Sahara Reporters ya bayyana cewa kasar Najeriya tayi wani babban rashi na daya daga cikin manyan kwamnadojin ta da ke yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a dajin Sambisa mai suna Laftanal Kanal A. E. Mamudu.

Majiyar ta mu dai har ila yau ta bankado mana cewa yau din nan ne dai babban kwamnantan ya rasu tare da wani matashin sojan ruwa yayin da suke wani sintiri a dajin na Sambisa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel