Nigerian news All categories All tags
Karya ga hukuma: Kotu ta ba Sanata Dino Melaye belin Naira dubu 100

Karya ga hukuma: Kotu ta ba Sanata Dino Melaye belin Naira dubu 100

Wata kotun tarayyar dake zaman ta a unguwar Maitama, garin Abuja, babban birnin tarayya ta baiwa Sanata Dino Melaye dake zaman dan majalisar dattijai dake wakiltar jihar Kogi da aka gurfanar a gaban ta bisa laifin sharara karya ga hukuma belin Naira dubu 100.

Tun farko dai an gurfanar da dan majalisar ne bisa laifuka biyu da suka hada da shararwa gwamnati karya wajen bayar da bayanai na cewar an kai masa hari a shekarar bara, zargin da Sanatan kuma ya karyata.

Karya ga hukuma: Kotu ta ba Sanata Dino Melaye belin Naira dubu 100

Karya ga hukuma: Kotu ta ba Sanata Dino Melaye belin Naira dubu 100

KU KARANTA: An gano gidajen alfarma 2 na Sanata Ekweremadu a Landan

Legit.ng ta samu cewa sai dai bayan da alkalin kotun ya saurari bayanai daga bakunan lauyoyin dukkan bangarorin sai ya dage karar tare da kuma belin Naira dubu 100 kafin a cigaba da gabatar da karar zuwa 16 da kuma 17 ga watan Mayu.

A wani labarin kuma, Wasu bayanan sirri da muka samu daga majiyar mu ta Sahara Reporters ta tabbatar da cewa an gano wasu gidajen alfarma masu tsadar gaske har guda biyu a birnin Landan na kasar Ingila mallakar mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu.

Gidajen dai kamar yadda muka samu daga ma'aikatar da ke kula da filaye ta kasar Ingila din dai gidajen na da adreshi ne karmar haka: "52 Aylestone Avenue, London, NW6 7AB da kuma Flat 4, Varsity Court, 44, Homer Street, London, W1H 4NW.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel