Nigerian news All categories All tags
Karin wa'adin shugabannin jam'iyya: APC ta haka kabarin binne kan ta - PDP

Karin wa'adin shugabannin jam'iyya: APC ta haka kabarin binne kan ta - PDP

- A ranar Talata ne jam'iyyar APC ta yanke shawarar kara wa'adin shekara guda ga zababbun shugabannin jam'iyyar na kasa

- Jam'iyyar PDP mai adawa ta ce wannan mataki da APC ta dauka tamkar haka kabarin da za a binne ta ne

- Sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya fadi hakan jiya a Abuja

A ranar Talata ne jam'iyyar APC ta bayyana cewar ta yanke shawarar yin karin wa'adin shekara guda ga zababbun shugabannin jam'iyyar na kasa, kamar yadda Legit.ng ta rawaito.

Sai dai jam'iyyar adawa ta PDP ta ce matakin da jam'iyyar APC din ta dauka raguwar dabara ce tare da kwatanta yin hakan da tamkar haka kabarin da za a binne jam'iyyar APC ne.

Karin wa'adin shugabannin jam'iyya: APC ta haka kabarin binne kan ta - PDP

Kola Ologbondiyan

Sakataren yada labaran jam'iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya sanar da hakan ga manema labarai jiya a Abuja.

Ologbondiyan ya ce 'yan Najeriya zasu kayar da APC a zaben shekarar 2019 duk da tsoratar da ya ce jam'iyyar ta yi.

KARANTA WANNAN: Jami'an tsaro sun hallaka wani gagararren barawon shanu a Zamfara mai suna 'janar Buhari'

Sakataren yada labaran ya ce karin wa'adin shugabannin ya sabawa kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC, kuma ya sabawa tsarin dimokradiyya.

"Ya kamata jama'a su zama shaida cewar jam'iyyar APC ba ta girmama doka ko tsarin dimokradiyya. Sun saba yiwa dimokradiyya da kundin mulki karan tsaye. Sun kara wa'adin shugabannin jam'iyyar su ta haramtacciyar hanya domin tsarin mulkin jam'iyyar ba haka ya tanada ba," a cewar Ologbondiyan.

Jam'iyyar PDP ta ce APC ta yiwa kanta lahani babba, abinda ya rage kawai ta saurari jana'izar ta da za a yi 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel