Najeriya na samun nasarori a fagen yaki da rashawa - Shugaba Buhari

Najeriya na samun nasarori a fagen yaki da rashawa - Shugaba Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya tana samun nasarori cikin yaki da rashawa da takeyi

- Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da tawagar yan kasuwar kasar Qatar da suka ziyarce shi a fadar Aso Villa

- Shugaba Buhari ya kuma kara da cewa tsare-tsaren tattalin arziki da gwamnatin sa ta shimfida ne ya fiddo Najeriya daga matsin tattalin arziki

A ranar Alhamis ne shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa na samun nasara a yaki da rashawa da ta keyi. Ya kara da cewa gwamnatin na sa tana bin doka da oda wajen yaki da rashawar.

Kamar yadda hadimin shugaban kasa na fanin kafafen yadda labarai ya sanar, Shugaban kasar ya fadi hakan ne a yayin wata ganawa da ya yi da yan kasuwan kasar Qatar karkashin jagorancin tsohon sarkin kasar, Sheikh Al-Thani a fadar Aso Villa.

Muna samun nasarori wajen yaki da rashawa a Najeriya- Buhari

Muna samun nasarori wajen yaki da rashawa a Najeriya- Buhari

Bayan ya nuna gamsuwar sa kan yadda masu saka jari ke tururuwa zuwa Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari ya alakanta nasarorin da kasar ke samu da tsare-tsaren gwamnatin sa na habbaka tattalin arzikin Najeriya.

KU KARANTA: Abin mamaki: Wai gawa ta aiko sako cikin laya daga barzahu a kasar Masar

Shugaba Buhari ya ce, "Tsarin da gwamnatin tarayya shine rage dogaro ga man fetur da kuma takaita siyo abinci daga kasashen waje wanda hakan ne ya fara janyo hankalin masu saka jari daga kasashen duniya zuwa Afirka.

"Kamar yadda ku ka sani, Najeriya ta fice daga matsin tattalin arziki da ya adabi kasar na tsawon shekaru da yawa kuma mun rubunya kudin da muke dashi a asusun ajiyar mu ta kasashen waje.

"Muna samun nasara wajen yaki da rashawa kuma muna habbaka gine-gine tare da bin doka da oda."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel