Nigerian news All categories All tags
A inganta kiwon lafiyar mu, a dawo da 'yan matan Dapchi - 'Yan Najeriya sun mayar da martani kan dawowar Yusuf Buhari

A inganta kiwon lafiyar mu, a dawo da 'yan matan Dapchi - 'Yan Najeriya sun mayar da martani kan dawowar Yusuf Buhari

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, wasu 'yan Najeriya suka mayar da martani dangane da rahoton dawowar Yusuf Buhari, dan shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya shafe makonni yana jinya a wani asibitin kasar waje.

A yayin da wasu ke taya murna sakamakon dawowar da daya tilo na Buhari, wasu ko suna rokon shugaban kasar ne akan ya tabbatar da dawo da 'yan matan Dapchi cikin koshin lafiya da 'yan ta'adda na Boko Haram ke garkuwa da su.

Yusuf Buhari tare mahaifin sa yayin sauka a fadar Villa

Yusuf Buhari tare mahaifin sa yayin sauka a fadar Villa

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, tsautsayi ya afkawa Yusuf Buhari tun a ranar 26 ga watan Dasumba na 2017, inda yayi hatsari akan Baburin sa na hawa da shafe tsawon lokuta yana jinya a asibitin Cedarcrest dake birnin Abuja kafin a fice zuwa wata kasar waje da shi da har yanzu fadar ba ta bayyana ta ba.

KARANTA KUMA: Majalisar wakilai ta juya baya ga Kayode Fayemi da mataimakin sa

'Yan Najeriya da dama dai sun soki gwamnatin shugaba Buhari, sakamakon gazawar ta na inganta harkokin kiwon lafiya a kasar nan da ya sanya jiga-jigan gwamnati da kuma masu hannu da shuni ba su neman lafiya a asibitocin cikin ta.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wasu 'yan Najeriya sun kuma soki ministan Labarai da al'adu na kasa, Alhaji Lai Muhammad, sakamakon wata shigar tufafi da yayi yayin ziyarar kungiyar kwallon kafa ta Realmadrid dake kasar Andalus, wanda suke ganin ya kunyata kasar nan a idon duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel