Nigerian news All categories All tags
APC ta samu karuwa da mutane 10,000 a jihar Edo

APC ta samu karuwa da mutane 10,000 a jihar Edo

- Mutane 10,000 sunyi tururuwa wajen komawa jam'iyyar APC a jihar Edo

- Cikin wanda suka sauya shekan har da wani jigo daga jam'iyyar PDP daga karamar hukumar Esan ta Yamma, Felix Akhabue

- Gwamna Obaseki ya yi alkawarin samar da kuri'u miliyan 1.2 a babban zaben 2019

A ranar Alhamis, Jam'iyyar APC reshen Jihar Edo ta samu karuwa yayin da ta karbi mutane 10,000 daga wasu jam'iyyun siyasa da ke jihar.

Cikin wanda suka sauya shekar zuwa APC har da wani jigo a jam'iyyar PDP na karamar hukumar Esan ta Yamma, Mista Felix Akhabue.

Sauya sheka: Mutane 10,000 sun rungumi tsintsiya a jihar Edo

Sauya sheka: Mutane 10,000 sun rungumi tsintsiya a jihar Edo

Akhabue dai yana daya daga cikin wanda ake bugun kirji dasu a jam'iyyar PDP a yankin Esan ta Yamma.

DUBA WANNAN: Safarar miyagun kwayoyi: NDLEA ta kama mutum biyu a filin jirgin sama na Kano Read

Wanda suka canja shekan sun bayyana wa duniya komawar su jam'iyyar ta APC ne a yayin da jam'iyyar ta fita cikin gari don yin kamfe gabanin zaben kananan hukumomi da za'a gudunar ranar asabar a jihar.

Ministan matasa da wasanni Barrista Solomon Dalung ya ce sauyin shekar da kuma gangamin kamfe din da aka gudanar alama ne da ke nuna cewa al'umma sunyi ban kwana d PDP a jihar.

A jawabin da ya yi wajen taron, Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya yi alkawarin samar wa APC kuri'u miliyan 1.2 a babban zaben 2019 mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel