Safarar mutane daga Najeriya ta karu tun da APC ta hau kan mulki - PDP

Safarar mutane daga Najeriya ta karu tun da APC ta hau kan mulki - PDP

- Jam'iyyar PDP ta ce tunda APC ta hau kan mulkin jihar Edo safarar mutane ta karu

- Babban lauyan jihar Edo ya danganta safarar mutane ga al'adar mutanen Edo

Jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP, ta jihar Edo ta yi Allah wadai da kakkausar sukar da gwamnatin jihar Edo ta yi akan yadda safarar haifaffun jihar Edo zuwa kasar Libya ta karu.

A jawabin da kakakin jam’iyyar PDP, Chris Nehikhare, ya fitar ya ce, babban lauyan jihar Edo Ferfesa Yinka Omorogbe yayi sukar.

Safarar mutane daga Najeriya ta karu tun da APC ta hau kan mulki - PDP

Safarar mutane daga Najeriya ta karu tun da APC ta hau kan mulki - PDP

PDP ta yi kaca-kaca da, babban lauyan kasar, Yinka Omorogbe, akan danganta safarar mutane ga al’adar mutanen jihar Edo.

KU KARANTA : An kashe mutane 3 a sabon hari da aka kai kauyen Katsina

“Wannan maganar kasakanci ne ga mutanen jihar Edo, kuma idan za a fadi gaskiya tunda jam’iyyar APC ta karbi karagar mulkin jihar Edo a shekaru goma da suka wuce, Safarar mutane ta karu,” inji kakakin jam’iyyar PDP.

Gazawar jam'iyyar APC wajen samar wa mutanen jihar aikin yi, da rashin cika alkwarran da suka yi wa mutanen jihar a lokacin yakin neman zabe yasa mutane cikin matsanancin hali.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel