Nigerian news All categories All tags
Trump ya nemi hadin kan Saudiyya da gamayyar kasashen Larabawa don murkushe Iran

Trump ya nemi hadin kan Saudiyya da gamayyar kasashen Larabawa don murkushe Iran

- Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya na son kasashen larabawa sun takurawa kasar Iran dan rage mata karfin iko a yankin Gabas ta tsakiya

- Donald Trump ya zargi kasar Iran da ta da zaune tsaye a yankin Gabas ta tsakiya

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya gana ta wayar tarho da yariman saudiya mai jiran Gado, Muhanmaad dan Salman, da jagoran hadaddiyar daular Larabawa Muhammad dan Zayyad.

Majiyoyin Fadar shugaban kasar Amurka wato White House sun bayyana cewa, Trump ya ja hankalin kasashen akan tayar da zaune tsaye da kasar Iran ke ci gaba da yi a yankunansu.

Trump ya nemi hadin kan Saudiyya da gamayyar kasashen Larabawa don murkushe Iran

Trump ya nemi hadin kan Saudiyya da gamayyar kasashen Larabawa don murkushe Iran

Trump yana son kasashen Larabawa su kasar wa kasar Iran takunkumi dan rage karfin ikon ta a yankin Gabsa ta tsakiya.

KU KARANTA : Mutane bakwai sun mutu ta sanadiyar musayar wuta tsakanin sojoji da mayakar kungiyar Boko Haram a tafkin Chad

Shugaban kasar Amurka ya gode wa yarimomin biyun bisa irin rawar da suke taka wa a kungiyar hadin kan kasashen larabawa.

Daga karshe, Donald Trump, ya kuma tattauna da su kan alakar kasuwanci da ci gaban tattalin arziki da ke tsakanin Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel