Nigerian news All categories All tags
Jihohi 9 kacal ne suke goyon bayan bawa kananan hukumomin 'yancin kansu - NULGE

Jihohi 9 kacal ne suke goyon bayan bawa kananan hukumomin 'yancin kansu - NULGE

- Kungiyar ma'aikatun kananan hukumomi (NULGE) tayi korafi kan yadda wasu jihohi ke jan jiki wajen amincewa da kudirin bawa kananan hukumomi yancin kansu

- Kungiyar ta ce jihohi tara ne kawai suka nuna goyon bayan su ga kudirin, jihohi guda biyu kuma sunyi watsi da batun baki daya

- Shugaban kungiyar na (NULGE) ya yi ikirarin cewa wasu gwamnonin na tursasawa yan majalisun jihohin su jan kafa kan batun amincewa da kudirin

Kungiyar ma'aikatun kananan hukumomi na Najeiya (NULGE) ta bayyana cewa a halin yanzu jihohi tara ne kawai suka nuna goyon bayan su game da yiwa kundin tsarin Najeriya garambawul don bawa kananan hukumomin yancin cin gashin kansu.

Jihohi 9 kacal ne suka amince da bawa kananan hukumomin 'yancin kansu - NULGE

Jihohi 9 kacal ne suka amince da bawa kananan hukumomin 'yancin kansu - NULGE

Shugaban kungiyar na kasa, Mista Ibrahim Khaleel ne ya furta hakan yayin da ya kira wani taron manema labarai ranar Laraba a Abuja.

KU KARANTA: Abin mamaki: Wai gawa ta aiko sako cikin laya daga barzahu a kasar Masar

Ibrahim yayin da galibin jihohin ke jan kafa game da batun wasu jihohi guda biyu sun fito karara sun bayyana rashin amincewar da kudirin garambawul din.

Kamar dai yada Khaleel ya bayyana, jihohin da suka amince da kudirin sune jihohin Kwara, Benuwe, Filato, Bauchi, Cross Ribas, Bayelsa da kuma Ondo, a gefe guda kuma jihohin Edo da Imo sunyi fatali da kudirin baki daya.

Khaleel ya zargi gwamnonin jihohin na Imo da Edo ya tursasa wa majalisun jihohin su kin amincewa da kudirin yayin da su kuma gwamnonin jihohin arewa maso yamma suka sanya yan majalisun jihar na su yin walawala wajen mayar da hankali kan kudirin.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta rushe hukumomin zabe na jihohin domin a cewar sa kawai suna cin karen su ne ba babaka ta hanyar kasancewa yan amshin gwamnonin jihohin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel