Nigerian news All categories All tags
Safarar miyagun kwayoyi: NDLEA ta kama mutum biyu a filin jirgin sama na Kano

Safarar miyagun kwayoyi: NDLEA ta kama mutum biyu a filin jirgin sama na Kano

- Jami'an hukumar yaki da masu fatauci da miyagun kwayoyi NDLEA ta kama mutane biyu dauke da kulin abubuwan da ake zargin hodar iblis ne

- Mutum na farko da aka kama an gano cewa ya hadiye kuli 127 na hodar iblis inda daga bisani zai shiga gida Najeriya ya fitar dashi ta hanyar bayan gida

- Dayar wanda aka kama kuma mace ce yar asalin jihar Delta da ta boye wani farin garri da ake zargin hodar iblis ne a kasar jakar ta

Hukumar yaki da masu fatauci da miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama mutane biyu a filin jirgin saman Aminu Kano tare da miyagun kwayoyi wanda kudin su ya dara naira miliyan hamsin.

Kwamandan hukumar na filin jirgin saman, Miista Ambrose Umoru ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wandanda ake zargi ga manema labarai a ranar Alhamis a Kano.

Safarar miyagun kwayoyi: NDLEA ta kama mutum biyu a filin jirgin sama na Kano

Safarar miyagun kwayoyi: NDLEA ta kama mutum biyu a filin jirgin sama na Kano

Ya ce anyi nasarar kama mutanen biyu ne a ranar 17 ga watan Fabrairun 2018 yayin da jami'an hukumar ke tatance fasinjoji da jirgin Ethiopian Airlines mai lamba ET 941.

DUBA WANNAN: PDP ba ta da sauran kima a idanun 'yan Najeriya - El-Rufai

Umoru ya ce daya daga cikin wanda ake zargin dan asalin karamar hukumar Indemili ta kudu ne da ke Jihar Anambra kuma an same shi dauke da kilogram 2.180 na hodar iblis.

"Mutumin mai sana'ar aski kuma dan kasuwa da ke zaune a birnin Kinshaha na kasar Jamhuriyar Congo ya tafi garin Bujumbura da ke Burundi inda ya hadiye kuli 127 na hodar iblis," inji Umoru.

Umoru ya kuma ce dayar matan da ake tuhuma mai shekaru 32 yar asalin kauyen Ibuse na karamar hukumar Oshimili na jihar Delta an kama ta da dauke ta kilogram uku wani farin garri da ake zargin hodar iblis ce.

"Ta boye shi ne a wani lungu na kasar jakar kayan ta," inji shi.

Umoru ya ce wanda ake tuhuma ta tafi Addis Ababa na ke kasar Ethiopia ne inda ta taho da abin da ta ke dauke dashi cikin jakar don kawo shi gida Najeriya amma jami'an hukumar sukayi nasarar cafke ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel