Nigerian news All categories All tags
'Yan sanda sun kama Sarki Sunusi 'na bogi na shafin Instagram

'Yan sanda sun kama Sarki Sunusi 'na bogi na shafin Instagram

- Yasanda sun kama matashin dake amfani da sunan sarki Kano a shafin Instagram

- Matashi mai amfani da suna sarkin Kano a shafin Instagram yana da mabiya fiye 200,000

Jami’an ‘yansandan jihar Kano sun kama wani matashi da yake karyar cewa shi Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ne a shafin Instagram.

Matashin mai shekara 20 yana da mabiya fiye da 200,000 a shafin sa na Instagram da yake amfani da sunan sarki Kano.

Wannan yasa kamfanin Instagram ta tantance sunan, sannan ta ba shi shudiyar alama.

'Yan sanda sun kama Sarki Sunusi 'na bogi na shafin Instagram

'Yan sanda sun kama Sarki Sunusi 'na bogi na shafin Instagram

Shafin dai ya kasance na sirri ne da sai an amince kafin ka fara bin sa duk da cewa yana da alamar tamntancewar.

KU KARANTA : Mutane bakwai sun mutu ta sanadiyar musayar wuta tsakanin sojoji da mayakar kungiyar Boko Haram a tafkin Chad

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano Musa Magaji Majiya, ya fadawa manema labaru cewa, binciken da suka gudanar akan matashin yasa su kama shi.

Musa Magaji, ya ce sarkin Kano yana cikin mutane bakwai da matashin ke amfani da sunayen su a shafin Instagram, wanda ya hada da wasu manyan 'yan kasuwa da manyan masu fada a ji.

'Yan sanda sun ce matashin da ake tuhuma ya samu mabiya a kalla miliyan uku a dukkanin shafukan bogin da ya bude na kafafen sada zumunta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel