Nigerian news All categories All tags
Allah ya kubutar da wata dalibar sakandiren Dapchi, ta ci wani al-washi

Allah ya kubutar da wata dalibar sakandiren Dapchi, ta ci wani al-washi

- Wasu daga cikin daliban makarantar sakandiren Dapchi da su ka samu kubuta yayin harin da aka kai makarantar su sun magantu

- Sun fadi yadda shugaban makarantar da wasu malamai su ka taimake su wajen sulalewa

- Za a mayar da daliban makarantar dake shekarar karshe wata makarantar sakandire dake Nguru inda zasu rubuta jarrabawar karshe

Harin da mayakan kungiyar Boko Haram su ka makarantar sakandiren 'yan mata dake Dapchi ya fara shafar harkar ilimi a yankin garin, musamman ga daliban da abin ya shafa.

Wasu dalibai biyar da suka samu tsira yayin da aka kai harin sun tattauna da jaridar The Cable, Legit.ng ta ci karo da labarin a jaridar Vanguard.

Daya daga cikin daliban, Maryam Mohammed Miko, 'yar shekara 15, ta a baya burinta ta zama ma'aikaciyar lafiya amma yanzu ta ci alwashin cewar babu abinda zai kara hada ta da makaranta balle ma a yi maganar cigaba da karatu.

Alkah ya kubutar da wata dalibar sakandiren Dapchi, ta ci wani al-washi

Daliban Dapchi

Wata dalibar, Amina Mohammadu, ta ce ita kam zata iya komawa makaranta amma ba zata koma makarantar sakandiren Dapchi ba.

KARANTA WANNAN: Dalilin karin wa'adin shekara guda ga shugabannin jam'iyyar APC - Oyegun

Da take bayar da dalilin da yasa ba zata koma makarantar sakandiren Dapchi ba, Amina, ta ce "ba zan iya komawa makarantar mu ba saboda kafin 'yan Boko Haram din su tafi da 'yan uwan mu sun fada mana cewar zasu dawo, sannan sun fada mana cewar basu san ma da makaranta a wurin ba, da tuni sun dade da kawo hari."

Yagana Mustapha ta ce sai an kawo tsaro makarantar sannan zata yarda ta koma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel