Nigerian news All categories All tags
Ba bu wata barazana da za ta firgita ni - Mahmood Abubakar

Ba bu wata barazana da za ta firgita ni - Mahmood Abubakar

A ranar Larabar da ta gabata ne, shugaban hukumar zabe ta kasa wato INEC, Farfesa Mahmood Abubakar, ya bayyana cewa tuni ya riga da wuce munzalin shiga tsaka mai wuya ko kuma firgicewa sakamakon wata barazana ko kalubale.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai na jaridar The Interview, inda yace ba ya da fargaba ta ko wane irin nau'i na barazana.

Farfesan ya bayyana hakan a sakamakon korafe-korafe dake kunno kai akan katukan zabe da kuma tuhumce-tuhumce na 'yan siyasa da cewar INEC ba ta da amincin gudanar da zabe na hakikanin gaskiya ba tare da magudi ba.

Farfesa Mahmood Abubakar

Farfesa Mahmood Abubakar

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, a kwana-kwanan nan ne gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa baiwa kananan yara damar kada kuri'un su a zaben jihar Kano ya bata sunan hukumar ta zabe a idon duniya baki daya, sakamakon yaduwa da hotunan suka yi a shafuka na sada zumunta.

KARANTA KUMA: Jihohi 35 ke rike da albashin ma'aikata - TUC

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar ta zabe ta kasa ta barrantar da kan ta dangane da zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar Kano, inda tace hurumin hukumar zaben jihar ne.

Sai dai Farfesa Yakubu ya kara da cewa, babu wani kalar Dare da Jemage bai gani ba, kuma babu wata barazana ko hura wuta da zata sanya ya kaucewa tsare-tsaren da doka ta gindaya.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kwamshinan lafiya na tsohuwar gwamnatin jihar Kano zai gurfana gaban alkali da laifin zamba ta N47.8m a ranar 8 ga watan Maris.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel