Nigerian news All categories All tags
Sanatoci da masu zanga-zanga sun raka Dino Melaye kotu

Sanatoci da masu zanga-zanga sun raka Dino Melaye kotu

- Magoya bayan Sanata Dino Melaye sun raka shi Kotu wurin sharia a Abuja

- Sanata Murray Bruce yana cikin sanatocin da suka raka Dino Melaye kotu

Sanatoci da kungiyar matasa magoya bayan, Sanata mai wakiltar mazabar Kogi West, Sanata Dino Melaye, sun raka shi kotun da za a yi masa sharia a safiyar ranar Laraba a Abuja.

A watan Fabrairu ne gwamnatin tarayya ta ofishin babban lauyan kasa (AGF) ta maka, sanata Dino Melaye a Kotu, akan yiwa shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Kogi, Edward Onoja, karyan cewa ya dauki nauyin kashe shi.

Sanatoci da masu zanga-zanga sun raka Dino Melaye kotu

Sanatoci da masu zanga-zanga sun raka Dino Melaye kotu

Ana tuhumar Dino Melyae da laifin yiwa 'yansanda karya.

KU KARANTA : Mutane bakwai sun mutu ta sanadiyar musayar wuta tsakanin sojoji da mayakar kungiyar Boko Haram a tafkin Chad

Magoya bayan na Dino, su na dauke da kwalaye da faska-faskan fastoci masu dauke da hotunan sa, kuma an rubuta: “Mu na bayan Dino Melaye” da manyan rubutu a jikin kowace babbar fasta.

Sanata Ben Bruce na jam’iyyar PDP daga jihar Bayelsa yana cikin Sanatocin da suka raka Dino Melaye kotu a safiyar ranar Alhamis.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel