Yaki da Boko Haram ya koma harkar Kasuwanci - Fayose

Yaki da Boko Haram ya koma harkar Kasuwanci - Fayose

Gwamnan jihar Ekiti Ayodel Fayose, yayi ikirarin cewa yaki da ta'addancin Boko Haram ya zamto hanyar samun riba ta wasu tsiraren mutane, inda suke amfani da damar su wajen wawuso tare da almundahanar kudaden talakawan Najeriya.

Gwamnan ya tabbatar da hasashen sa da cewa, yaki da ta'addancin Boko Haram ya zamto harkar kasuwanci sakamakon wasu mutane dake ribatar yashe dukiyoyi na musamman da aka tanada domin 'yan gudun hijira da kuma makudan kudaden fansa domin ceto wadanda 'yan ta'adda ke garkuwa da su.

Fayose yake cewa, ire-iren wannan mutane ba za su so ganin karshen wannan ta'addanci ba a fadin kasar nan.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, cire dakarun Soji daga garin Dapchi kwanaki kadan kafin yashe dalibai 110 wani tuggu ne da aka kulla kasar nan.

Gwamnan jihar Ekiti; Ayodele Fayose

Gwamnan jihar Ekiti; Ayodele Fayose

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, gwamna Fayose cike yake da mamakin yadda har yanzu babu wanda aka titsiye kan afkuwar wannan lamari duk da sabanin rahotanni ma suu cin karo da juna na jami'an 'yan sanda da Dakarun Sojin kasar nan.

KARANTA KUMA: Kwamishinan Kwankwaso zai gurfana gaban Alkali da laifin Zambar N47.8 a ranar 8 ga watan Maris

Fayose cikin damuwa da takaici ya kara da cewa, alamu sun nuna cewa Najeriya ba za ta ga karshen ta'addancin Boko Haram anan kusa ba, sakamakon ci gaba da zaman jiran shugaba Buhari na ceto 'yan Kasar ba wani abu bane face bata lokaci.

A kalaman sa, gwamnatin shugaba Buhari ta cika baki na kawar da ta'addancin Boko Haram cikin watanni ukun farko na shugabancin ta, sai dai kawowa yanzu sama watanni talatin abu yaki ci yaki cinyewa.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wasu 'yan Najeriya sun soki Ministan Labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammad, sakamakon wata shigar tufafi da ya yi yayin ziyarar kungiyar kwallaon kafa ta Realmadrid a can kasar Andalus.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel