Nigerian news All categories All tags
Mutane bakwai sun mutu ta sanadiyar musayar wuta tsakanin sojoji da mayakar kungiyar Boko Haram a tafkin Chad

Mutane bakwai sun mutu ta sanadiyar musayar wuta tsakanin sojoji da mayakar kungiyar Boko Haram a tafkin Chad

- Harin kuna bakin wake yayi sandaiyar mutuwar sojoji biyu a tafkin Chad

- Kanal Oyema yace sojoji sun kashe mayakan Boko haram guda biyar

Sojoji biyu sun mutu ta sanadiyar raunin da suka samu daga harin kuna bakin wake na kungiyar Boko Haram ya kai musu a ranar Talata.

Kafin harin kuna bakin wake, sojojin sun kashe mayakan Boko Haram guda biyar a tafkin Chadi a attisayen Deep Punch da suke gudanar wa a yankin.

Mutane bakwai sun mutu ta sanadiyar musayar wuta tsakanin sojoji da mayakar kungiyar Boko Haram a tafkin Chad

Mutane bakwai sun mutu ta sanadiyar musayar wuta tsakanin sojoji da mayakar kungiyar Boko Haram a tafkin Chad

Mai magana da yawun bakin rundunar Attisayen Lafiyaj Dole, Kanal Onyema Nwachukwu, ya bayyana haka a daren ranar Laraba.

KU KARANTA : A daina yi wa jarirai wanka da ruwan zafi da zaran an haihu - Helen Bulu

Kanal Onyema, yace sojoji suna cikin tafiyar wani dan kuna bakin wake ya kai wa motar dake dauko musu man fetur hari.

“Amma duk da haka sojojin mu sun samu nasarar rusa sansanin mayakan Boko Haram da dama Sambisa da Tafkin Chadi,” Inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel