Nigerian news All categories All tags
INEC da hukumar kidaya za su cire sunayen matattu daga rajistar zabe

INEC da hukumar kidaya za su cire sunayen matattu daga rajistar zabe

- Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahood Yakubu ya kai ofishin hukumar Kidaya NPC ziyara a Abuja

- INEC ta nemi hadin kan hukumar kidaya wajen cire sunayen matattu daga rajista

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta nemi hadin kan hukumar Kidaya ta kasa (NPC) da ta bata sunayen mutanen da suka mutu daga 2015 zuwa yanzu, domin cire su daga cikin rajistar INEC.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahood Yakubu, yayi wannan kira a lokacin da ya kai wa shugaban hukumar Kidaya, Eze Durulheoma ziyara a ofishin sa dake birnin Abuja.

INEC da hukumar kidaya za su cire sunayen matattu daga rajistar zabe

INEC da hukumar kidaya za su cire sunayen matattu daga rajistar zabe

Shugaban hukumar NPC, Eze Durulheoma, ya tabbatar wa, Farfesa Mahood Yakubu,cewa hukumar sa za ta baiwa INEC hadin kai sosai.

KU KARANTA : 'Yan Najeriya sun soki Ministan Labarai kan wata shiga a kasar Andalus

Eze yace, da zaran sun kammala tantance duka sunayen mutanen da suka mutu a fadin kasar, za su damka wa hukumar INEC sunayen.

Yakubu ya ce INEC za ta yi iya kokarin ta wajen tabbabar da zaben 2019 ya yi nasara sosai kuma an gudanar da shi a bisa turbar adalci, kuma ya kasance sahihi, ba tare da tashin-tashina ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel