Nigerian news All categories All tags
Saraki ya bukaci majalisun dokoki na jiha da su dakatar da kudaden fansho na tsoffin gwamnoni da mataimakansu

Saraki ya bukaci majalisun dokoki na jiha da su dakatar da kudaden fansho na tsoffin gwamnoni da mataimakansu

Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya bukaci dukannin jihohin tarayya da su daina biyan kudaden fasho ga tsofaffin gwamnonin jihohinsu.

Domin cimma haka, a jiya, Saraki ya bukaci dukannin majalisun dokoki na jiha da su dauki darasi daga jihar Kwara sannan su fitar da nasu dokar hana biyan fansho ga tsoffin gwamnoni da mataimakan gwamnoni.

Gwamnatin jihar Kwara ta kafa wannan doka a ranar Talata.

Saraki ya bukaci majalisun dokoki na jiha da su dakatar da kudaden fansho na tsoffin gwamnoni da mataimakansu

Saraki ya bukaci majalisun dokoki na jiha da su dakatar da kudaden fansho na tsoffin gwamnoni da mataimakansu

A wani jawabi da aka fitar a jiya, Saraki ya yaba ma kakakin majalisar dokokin jihar, Ali Ahmad, kan aiki da yayi na gabatar da dokar.

KU KARANTA KUMA: Yusuf Buhari ya sadu da mahaifinsa bayan dawowa daga hutun jinya (hotuna)

Saraki ya kasance gwamnan jihar Kwara tsakanin 2003 da 2011.

A halin yanzu mun samu labari ba da dadewa ba cewa Majalisar Dattawa za ta binciki Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello game da zargin da ke kan sa na yin rajistar katin zabe fiye da sau daya wanda hakan haramun ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel