Nigerian news All categories All tags
PDP ba ta da sauran kima a idanun 'yan Najeriya - El-Rufai

PDP ba ta da sauran kima a idanun 'yan Najeriya - El-Rufai

- Gwamna El-Rufai ya kwatanta PDP a matsayin hajjar da kowa kyamar tayawa balle ya saya

- Gwamnan ya ce yan Najeriya sun gaji da PDP shi yasa suka hambare ta a shekarar zaben 2015

- Gwaman ya ce abin al'ajabi ne yadda aka kafa APC shekara daya gabanin zabe kuma ta kayar da PDP da tayi shekaru 15 tana mulki

Gwaman Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ba ta da sauran kima ko daraja a idanun yan Najeriya.

Gwaman ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da wata kasida a jami'ar Al-Hikma da ke garin Ilorin na jihar Kwara.

PDP ba ta da sauran kima a idanun 'yan Najeriya - El-Rufai

PDP ba ta da sauran kima a idanun 'yan Najeriya - El-Rufai

A cewar El-Rufai, barnar da jam'iyyar ta PDP ta kwashe shekaru 15 tana tafka wa za su kara bayyana ga al'umman Najeriya kafin zaben 2019.

KU KARANTA: Za'a hukunta masu yadda kalaman kiyaya ta hanyar rataye - Majalisar Dattawa

Ya kuma bayyana nasarar da jam'iyyar ta APC ta samu a matsayin abin al'ajabi duba da yadda aka kafa APC shakara daya kafin zabe amma da kayar da jam'iyyar da ta shafe shekaru 15 tana mulkin Najeriya.

"Yan Najeriya sun hambare PDP daga mulki ne don sun gaji ta ita, kowa ya fahimce cewa jam'iyyar ta PDP za ta kai Najeriya ga halaka ne kawai shiyasa aka hambare su," inji shi.

Daga karshe El-Rufai ya yaba da kwamitin sulhu da aka kafa karkashin jagorancin Asiwaju Bola Tinubu, ya kuma ce ya yi imanin cewa kwamitin zai kawar da dukkan matsalolin da ke addabar jam'iiyar kuma za su samu nasara a zabe mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel