Nigerian news All categories All tags
Yaki da rashawa: Yadda wani tsohon minista ya lakume naira miliyan 840 cikin yan watanni

Yaki da rashawa: Yadda wani tsohon minista ya lakume naira miliyan 840 cikin yan watanni

A cigaba da shari’ar da gwamnatin tarayya, ta hannun hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ke yi da tsoffin ministoci, Femi Fani Kayode da Nenadi Usman kan zargin satar kudi, an cigaba da tone tonen asiri.

Sahara Reporters ta ruwaito a zaman Kotun na ranar Laraba 28 ga watan Feburairu, wani shaida da hukumar EFCC ta kawo, kuma ma’aikacin bankn Zenith, Teslim Ajuwon ya bayyana yadda tsohon ministan sufurin jirgin sama, Fani Kayode ya bude asusun banki a watan Feburairu na shekarar 2015.

KU KARANTA: Ta leƙo ta koma: Amarya ta fasa auren Angonta bayan ta gane yana da sanƙo kwana ɗaya kafin ayi biki

Shaidan ya bayyana cewa a daga ranar 2 ga watan Feburairu zuwa watan Maris, an sanya naira miliyan 840 a asusun, zubi uku, amma zuwa ranar 31 ga watan Yuli, har an kwashe kudaden gaba daya, babu da ya ragu sai 189,402 kacal.

Yaki da rashawa: Yadda wani tsohon minista ya lakume naira miliyan 840 cikin yan watanni

Kayode

Majiyar Legit.ng ta ruwaito tsohon ministan ya cire naira miliyan 10, sau da yawa, wanda hakan ya saba ma dokar banki, da ta kayyade iyakar cire naira miliyan 5 ga mutum a kowanne rana, kamar yadda shaidan ya tabbatar.

Sai dai lauyan wanda ake kara, Norrison Qaukers ya musanta sahihancin rahoton asusun bankin da shadain ya karanta, a nan ne kuma shi ma shaidan ya zargi lauyan wanda ake kara da cewa suna kokarin yi masa barazana da rayuwarsa don ya bayyana wadannan bayanai.

Yaki da rashawa: Yadda wani tsohon minista ya lakume naira miliyan 840 cikin yan watanni

Nenadi

EFCC na tuhumar Fani Kayode, Nenadi Usman, tsoho shugaban karamar hukumar Kagarko, Yusuf Danjuma, tare da wasu kamfanoni guda biyu kan zargin karkatarwa tare da yin sama da fadi da kudi naira biliyan 4.6.

Bayan sauraron dukkanin bangarori, sai Alkalin Kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar Alhamis 1 ga watan Maris.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel