Nigerian news All categories All tags
Ana zargin wasu Jami’an Gwamnati 3 da sace kayan da aka kawowa ‘yan gudun hijira

Ana zargin wasu Jami’an Gwamnati 3 da sace kayan da aka kawowa ‘yan gudun hijira

- Hukumar EFCC ta maka Shugaban Hukumar SEMA a gaban Kotu

- Ana zargin Ma’aikatan SEMA na Jihar Gombe da sace kayan IDP

- Yanzu Alkali Abubakar Jauro ya dage karar har sai cikin watan Afrilu

Mun samu labari daga Daily Trust cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta damke Jami’in bada agajin gaggawa da yayi gaba da kayan ‘Yan gudun hijira inda yanzu har an shiga Kotu.

An zargin wasu Jami’an Gwamnati 3 da sace kayan da aka kawowa ‘yan gudun hijira

Ma’aikatan SEMA sun dauke siminti na masu gudun hijira

Ana zargin Shugaban da wasu Jami’an Hukumar SEMA mai bada agajin gaggawa a Jihar Gombe Danlami Arabs Rukuje da karkatar da kayan Bayin Allah da ke sansanin gudun hijira. Yanzu haka dai an dage shari’ar sai Afrilu.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram da su kayi ridda sun kammala karatu

EFCC na karar Rukuje da ma’aikatan da ke tsare dakin ajiyar kayan da sace wasu kayan gini na ‘yan gudun hijira. Kayan da aka sace sun hada da buhunan siminti 5000 da kayan fenti da sauran kayan da aka kawo domin jama’an.

Kwamitin da Shugaban kasa Buhari ya nada domin kula da mutanen da ke gudun Hijira a Yankin Arewa maso gabas ne ta kawowa Hukumar wannan kaya amma aka sace. Yanzu dai wadannan Ma’aikata su na neman Kotu ta ba su beli.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel