Nigerian news All categories All tags
Dalilin karin wa'adin shekara guda ga shugabannin jam'iyyar APC - Oyegun

Dalilin karin wa'adin shekara guda ga shugabannin jam'iyyar APC - Oyegun

- Shugaban jam'iyyar APC na kasa, John Oyegun, ya bayyana cewar jam'iyyar APC ta yanke shawarar kara wa'adin shugabannin ta ne domin gujewa fadawa cikin rigingimun siyasa

- Oyegun ya ce ba dukkan 'ya'yan jam'iyyar ne su ka yarda da matakin da jam'iyyar ta dauka ba

- Ya ce za a iya kiyaye afkuwar rigingimun cikin gida ta hanyar yin karin wa'adin ga shugabannin jam'iyyar

A jiya ne Legit.ng ta kawo maku, a daya daga cikin labaran ta, cewar jam'iyyar APC ta yanke shawarar kara wa'adin shekara guda ga zababbun shugabannin jam'iyyar na kasa.

A wata ganawa da ya yi da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa na jam'iyyar, shugaban jam'iyyar APC, John Oyegun, ya ce jam'iyyar ta dauki wannan mataki ne saboda dumbin aiyukan dake gaban ta a cikin shekarar nan.

Dalilin karin wa'adin shekara guda ga shugabannin jam'iyyar APC - Oyegun

Oyegun

Wa'adin shugabannin jam'iyyar APC zai kare ne ranar 30 ga watan Yuni na shekarar nan kafin sanar da yin karin wa'adin.

DUBA WANNAN: Majalisar zartarwar APC ta musanta ayyana Buhari a matsayin dan takarar jam'iyyar

"Za mu fuskanci zabukan fitar da 'yan takarar gwamna a jihohin Ekiti da Osun da 'yan majalisun jihohi da na tarayya da sauran su," inji Oyegun.

Oyegun ya kara da cewa "Hakan ne ya sa muka ga zai fi dacewa mu jinkirta yin zaben sabbin shugabanni domin ragewa kan mu wahala da kuma gudun duk wani abu da kan iya kawo rabuwar kai tsakanin 'ya'yan jam'iyyar mu a wannan lokaci da muke matukar bukatar hadin kan kowa da kowa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel