Shugaba Buhari ya rufe taron farfado da tafkin chadi a Abuja

Shugaba Buhari ya rufe taron farfado da tafkin chadi a Abuja

- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci kasashen dake makwabtaka da tafkin chadi a taron da aka yi na farfado da tafkin, wanda aka gudanar a Abuja.

- Ya bukaci a tabbatar an shirya tsarin farfado da tafkin cikin tsari

- Ya bayyana muhimmancin tafkin wanda kasashen Afrika da dama suke karuwa da albarkar shi

Shugaba Buhari ya rufe taron farfado da tafkin chadi a Abuja

Shugaba Buhari ya rufe taron farfado da tafkin chadi a Abuja

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci kasashen dake makwabtaka da tafkin chadi a taron da aka yi na farfado da tafkin, wanda aka gudanar a Abuja.

DUBA WANNAN: Saura kadan a sanya hannu akan kudurin rage shekarun tsayawa takara - Not too young to run

A wurin karon Shugaba Buhari ya bukaci a tabbatar an shirya tsarin farfado da tafkin cikin tsari, ba wai sai an gama taron ba kuma maganar ta zo ta warware. Ya bayyana muhimmancin tafkin wanda kasashen Afrika da dama suke karuwa da albarkar shi.

Sannan ya tunatar da su yadda kafewar tafkin ya kawo matsalolin zamantakewa na ayyukan cigaban tattalin arzikin yankin, musamman ma ga manoma.

Shugaban yayi kira ga babban bankin duniya, da bankin musulunci da manyan kungiyoyi dake kula rayuwar al'umma su bada himma domin tabbatar da an dauki kwararan matakan da suka kamata wurin farfado da tafkin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel