Nigerian news All categories All tags
Saura kadan a sanya hannu akan kudurin rage shekarun tsayawa takara - Not too young to run

Saura kadan a sanya hannu akan kudurin rage shekarun tsayawa takara - Not too young to run

- Kungiyar matasan Najeriya ta kusa cimma burinta

- Kungiyar ta samu hadin kan majalisar tarayya da ta jihohi wanda dokar kasa ta tanada kafin kundin tsarin kasar ya amince da kudurin rage shekarun takara

- Yanzu kawai shugaba Buhari ya rage ya rattaba hannu, dokar ta tsaya

Saura kadan a sanya hannu akan kudurin rage shekarun tsayawa takara - Not too young to run

Saura kadan a sanya hannu akan kudurin rage shekarun tsayawa takara - Not too young to run

Kungiyar matasa ta Najeriya wacce take kokarin ganin an bawa matasa damar tsayawa takaran mukaman siyasa, daga kan dan shekara 18 zuwa sama, ta kusa cimma burimta.

DUBA WANNAN: Bayan babban taron APC na kasa: 'Buhari ne dan takarar mu a 2019'

Kudurin kungiyar ya samu karbuwa a wajen majalisun dokokin kasar nan. Baya ga samun hadin kan majalisar tarayya, kungiyar ta samu hadin kan majalisar jihohi sama da 24 wanda dokar kasa ta tanada kafin kundin tsarin kasar ya amince da kudurin rage shekarun. Kungiyar ta samu jihohi 31.

Samun nasarar kungiyar akan jihohi 31, shine ya kawo kungiyar fagen karshe, wanda yake nuni da shugaban kasa kawai ake jira ya saka hannu ga kudurin, inda yin hakan zai mai da kudurin ya zama doka.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar matasan Mike Amanza ya yi jawabi akan yawan shekarun da kudurin ya kunsa. Inda yace idan har gwamnati ta kafa dokar duk mai shekaru 25 zai iya fitowa takarar majalisar jiha ko ta tarayya. Sannan dan shekaru 35 zai iya fitowa takarar shugaban kasa ko gwamna.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel