Nigerian news All categories All tags
Aisha Buhari ta godema yan Najeriya bisa addu’ansu ga danta Yusuf a lokacin da yake jinya

Aisha Buhari ta godema yan Najeriya bisa addu’ansu ga danta Yusuf a lokacin da yake jinya

- Aisha Buhari ta saki wani jawain godiya ga yan Najeriya kan addu’’ansu ga danta, Yusuf a lokacin da yake jinya bayan anyi masa aiki a kasar waje

- Yusuf Buhari yayi hatsari tare da abokinsa, Bashir Gwandu a Gwarimpa, Abuja

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari tayi magana a karo na farko tun bayan lokacin da danta na fari, Yusuf ya dawo Najeriya bayan hatsari da yayi akan babur wanda ya ji masa rauni a kai a ranar 26 ga watan Disamba, 2017 a Abuja.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, a ranar Alhamis, 1 ga watan Maris, uwargidan shugaban kasar tayi godiya ga kowa kan fatan alkhairi da addu’o’insu tun bayan afkuwar hatsarin.

Ta ce: “Mungode Allah da dawowar Yusuf danmu a yau bayan tafiya jinya. Da ya sauka a filin jirgin sama ya samu tarba daga ministan lafiya Dr. Osagie, yayinda a fadar shugaban kasa yan uwa, uwargidan mataimakin shugaban kasa, ministan cikin gida, Gwamna Yahaya Bello da hadimai suka tarbe sa a fadar shugaban kasa.

“A madadin yan uwa ina nuna godiyarmu ga addu’o’i da fatan alkhairinku tun bayan afkuwar hatsarin. Allah ya yi albarka ya ci gaba da yi mana jagora.”

A baya Legit.ng ta kawo cewa Dan shugaban kasa, Muhamadu Buhari, Yusuf, ya dawo Najeriya a ranar Litinin bayan ya jinya a kasar waje.

KU KARANTA KUMA: Yusuf Buhari ya sadu da mahaifinsa bayan dawowa daga hutun jinya (hotuna)

Yusuf Buhari, ya samu lafiya sosai, kuma zai cigaba da rayuwar sa kamar yadda ya saba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel