Nigerian news All categories All tags
Majalisar zartarwar APC ta musanta ayyana Buhari a matsayin dan takarar jam'iyyar

Majalisar zartarwar APC ta musanta ayyana Buhari a matsayin dan takarar jam'iyyar

- Shugabancin jam'iyyar APC na kasa ya ce bai ayyana shugaba Buhari a matsayin dan takarar shugaba kasar jam'iyyar a 2019

- Sakataren watsa labaran jam'iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce basu tattauna batun takarar shugaban kasa ba a taron jam'iyyar na jiya

- Jam'iyyar ta ce ta bayyana cewar ta yarda da nagartar Buhari ba yana nufin ta tsayar da shi a matsayin dan takarar ta ba

Shugabancin jam'iyyar APC na kasa ya bayyana cewar basu tsayar da shugaba Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ba a zaben shekarar 2019.

Sakataren watsa labaran jam'iyyar APC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewar taron da uwar jam'iyyar ta yi a jiya bai tattauna batun takarar shugabancin kasa ba.

Majasilar zartarwar APC ta musanta ayyana Buhari a matsayin dan takarar jam'iyyar

Majasilar zartarwar APC ta musanta ayyana Buhari a matsayin dan takarar jam'iyyar

Kazalika uwar jam'iyyar ta kasa ta ce kalaman ta na amincewa da nagartar shugaba Buhari ya tsaya takara a zaben shekarar 2019 ba yana nufin jam'iyyar ta tsayar da shi a matsayin dan takarar ta ba ne.

DUBA WANNAN: An tafka kazamin rikici tsakanin 'yan kungiyar asiri da jami'an tsaro a Legas

Abdullahi na furta wadannan kalamai ne a wata hira ta wayar tarho da jaridar Punch, kamar yadda ta wallafa.

A jiya ne kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewar wasu shugabannin jam'iyyar APC da ba a ambaci sunan su ba sun tabbatar da zabin shugaba Buhari a matsayin dan takarar jam'iyyar a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel