Nigerian news All categories All tags
Rikicin APC: ‘Dan Majalisar PDP yayi ba’a ga Sanatocin APC

Rikicin APC: ‘Dan Majalisar PDP yayi ba’a ga Sanatocin APC

- Kwanan nan Jam’iyyar APC tayi wani babban taron ta na N.E.C

- Ahmad Lawan ya nemi a dage zaman Majalisa ranar saboda taron

- Sanatan PDP ya tsokani APC kan rikicin da ke faruwa a Jam'iyyyar

Mun samu labari cewa a makon nan ne wani ‘Dan Majalisun PDP yayi wa Takwaran su na APC shakiyanci a lokacin da ake wani zama bayan sun nemi a ba su dama su halarci taron Jam'iyya.

Wani ‘Dan Majalisar PDP ya tsokani Sanatocin APC a zaman Majalisa

Wani 'Dan Majalisar PDP yayi ba’a ga rikicin APC

Shugaban Sanatoci masu rinjaye a Majalisar watau Sanata Ahmad Lawan ya nemi a dage zaman da aka shirya a Majalisar saboda ‘Yan Jam’iyyar sa ta APC su na da wani taro na musamman a ranar da su ka shirya gudanarwa a Abuja.

KU KARANTA: An nemi Saraki an rasa wajen taron APC da aka yi

Ahmad Lawan ya nemi Mataimakin Shugaban Majalisar Ike Ekweremadu ya ba ‘Yan Jam’iyyar su damar halartar taron Majalisar zartawa ta NEC. Wani ‘Dan Majalisar Emmanuel Bwacha da ke Jam’iyyar PDP yayi na’am da wannan roko.

Sanata Bwacha ya tsokani Abokan aikin na sa na APC inda yace ‘Yan Sandan da aka jibge a wajen taron ganin irin rikicin da ake yi a Jam’iyyar ta APC sun yi kadan. Sanatan yace yana addu’a ‘Yan APC su iya yin wannan taro su gama lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel