Nigerian news All categories All tags
Matashi ya yi tsirara haihuwar uwarsa a cikin Masallaci, ya yi matashin kai da Al-Qur’ani a Zamfara

Matashi ya yi tsirara haihuwar uwarsa a cikin Masallaci, ya yi matashin kai da Al-Qur’ani a Zamfara

Kai jama’a, wai menene bukatar mutanen zamanin nan ne? Arziki, aure, yaya, ilimi, suna, ko me? Saboda a gaskiya yadda mutane ke kauce hanya domin son zuciyarsu, a iya cewa ko a zamanin jahiliyya sai haka.

Shafin Rariya dake kafar sadarwar zamani na Facebook ta kawo mana rahoton wani matashi mai tsananin son duniya da aka kama shi cikin wani mummunan hali a wani Masallaci dake jihar Zamfara.

KU KARANTA: Rikicin jihar Kaduna: An banka ma gidajen wani kauye wuta

Wannan abu mara dadin ji ya faru ne a garin Mada na jihar Zamfara, inda aka cafke wannan matashi da ba’a bayyana sunansa ba yana kwance tsirara a cikin Masallaci, sa’annan ya yi matashin kai da Al-Qur’ani mai tsarki, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Matashi ya yi tsirara haihuwar uwarsa a cikin Masallaci, ya yi matashin kai da Al-Qur’ani a Zamfara

Matashin

Majiyar ta kara da cewa matasan garin Mada sun kama wannan matashi cikin wannan hali ne a daren talata, 27 ga watan Feburairu,wayewar garin Laraba.

Jama’an da suka kama shi, sun bayyana cewa mutumin dan asalin garin Gusau ne, babban birnin jihar Zamfara, sa’annan sun lakada masa dan banzan duka, kuma suka daure shi tamau, daurin huhun goro a jikin wani falwaya.

Allah ya sa mufi karfin zuciyanmu a ko da yaushe, kuma Ya bamu wadatan zuci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel