Nigerian news All categories All tags
An tafka kazamin rikici tsakanin 'yan kungiyar asiri da jami'an tsaro a Legas

An tafka kazamin rikici tsakanin 'yan kungiyar asiri da jami'an tsaro a Legas

- Kimanin mutane biyar, ciki har da wani dan sanda, su ka rasa ran su a wani rikici tsakanin 'yan kungiyar asiri da jami'an tsaro

- Rikicin ya faru ne a unguwar Idi-Oro dake Legas kuma ya yi sanadiyar mutuwar wasu tare da raunata jama'a da dama

- Sai da hukuma ta yi amfani da 'yan sanda na musamman (RRS) sannan aka shawo kan rikicin

Wani kazamin rikici da ya barke tsakanin 'yan kungiyar asiri da jami'an a unguwar Idi-Oro dake Legas ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane biyar.

Rikicin ya ritsa da wasu mutum biyu 'yan kasuwar kasa da kasa ta Ladipo dake jihar Legas. Kazalika 'yan kungiyar asirin sun caccakawa wani mutum wuka sakamakon barkewar rikicin.

An tafka kazamin rikici tsakanin 'yan kungiyar asiri da jami'an tsaro a Legas

Jami'an tsaro

Rahotanni sun bayyana cewar rikicin ya barke ne biyo bayan gano wata maboyar 'yan kungiyar asirin da 'yan sandan gundumar D su ka yi a yankin Muhsin.

An fara gwabzawa tsakanin jami'an 'yan sanda da 'yan kungiyar asirin tun ranar Talata kuma rikicin ya tsallaka har ranar Laraba.

KARANTA WANNAN: Harbin bindiga domin murnar biki ya aika ango barzahu

Su dai 'yan kungiyar asirin sun far wa har jama'ar da ba jami'an tsaro ba a wani yanayi da a kan iya kwatantawa da haushin kaza huce kan dami.

Jaridar The Nation cewar rikicin bai kwanta ba sai da hukuma ta yi amfani da 'yan sanda na musamman (RRS).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel