Nigerian news All categories All tags
Ana biyan Ma’aikatan iska albashin sama da Biliyan 3.5 a Jihar Benuwe

Ana biyan Ma’aikatan iska albashin sama da Biliyan 3.5 a Jihar Benuwe

- Gwamnatin Jihar Benuwe ta kara gano wasu ma’aikatan bogi

- Wani kwararren Ma’aikacin Gwamnati ne yayi wannan aiki

- An cire sunayen ma’aikatan karya da ke lashe albashin awuf

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an bankado wata badakala ta sama da Naira Biliyan uku da rabi a cikin harkar ma’aikatan Gwamnatin Jihar Benuwe kwanan nan.Yanzu haka dai an cire ma’aikatan bogi daga sahun masu karbar albashi a Jihar.

Ana biyan Ma’aikatan iska albashin sama da Biliyan 3.5 a Jihar Benuwe

Gwamna Ortom ya gano wata badakala a Jihar Benuwe

Gwamnatin Jihar karkashin Samuel Ortom na kokarin tantance ma’aikatan Jihar domin gano masu karbar albashi da sunan bogi. Yanzu haka dai wani tsohon Ma’aikacin Gwamnati Tersegha Ikyaabo ya mikawa Gwamnan binciken da yayi.

KU KARANTA: Majalisa ta nemi a hana biyan Gwamnoni kudin banza

A binciken da Tersegha Ikyaabo yayi, an gano cewa akwai badakalar Biliyan 3.514 da ake biyan ma’aikatan bogi a Ma’aikatu 7 na Jihar. An gano ma’aikata sama da 8,900 na karya da aka rika narkawa albashi daga tsakiyar 2015 zuwa 2017.

Ma’aikatun da aka gano wannan ma’aikatan na bogi sun hada da Makarantar koyon harkar noma ta Akperan Orshi, da kuma wata makarantar kwas na musamman da ke Makurdi da Kwalejin ilmi da ke Katsina Ala da ta Garin Oju da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel