Nigerian news All categories All tags
Oyegun: APC ba za ta kai labari ba bayan 2019 inji jigon Jam'iyyar

Oyegun: APC ba za ta kai labari ba bayan 2019 inji jigon Jam'iyyar

- Timi Frank yayi tir da batun kara wa'adin Shugaban Jam'iyyar APC

- Frank yace bai dace a kara wa'adin Shugaba John Oyegun ba a ka'ida

- Babban 'Dan Jam'iyyar yace hakan ya nuna APC ba za ta kai labari ba

Mun samu labari daga Jaridun kasar nan cewa wani babba a Jam'iyyar APC Timi Frank yayi kaca-kaca da Jam'iyyar mai mulki na kara wa'adin Shugaban Jam'iyyar Cif John Odigie Oyegun da 'Yan Majalisar sa yace ya saba doka.

Oyegun: APC ba za ta kai labari ba bayan 2019 inji jigon Jam'iyyar

Timi Frank yace bai kamata NEC ta kara wa'adin Oyegun ba

Tiki Frank wanda babba ne a APC yace Majalisar zartarwa ta NEC ta APC ta ba Jama'a kunya na kara wa'adin Majalisar gudanarwa watau NWC na Jam'iyyar karkashin Shugaban ta na kasa John Oyegun yace akwai son zuciya.

KU KARANTA: Majalisa za ta takawa Shugaban kasa Buhari burki

Frank yace hakan ya sabawa ka'ida ya kuma karya dokokin cikin gida na Jam'iyyar APC. Timi Frank yace sam bai kamata a kara tsawon wa'adin Shugaban Jam'iyyar ba domin ta tabbata bai san abin da yake yi ba a kujerar ta sa.

Har yanzu rikicin Jam'iyyar dai bai kare ba inda Frank yace ba a yi wa tsofaffin 'Yan PDP adalci a Jam'iyyar. Frank yace da karfi da yaji Bukola Saraki da Yakubu Dogara su ka karbi kujerar su na Shugabannin Majalisa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel