Nigerian news All categories All tags
Jihohi 35 ke rike da albashin ma'aikata - TUC

Jihohi 35 ke rike da albashin ma'aikata - TUC

Kungiyar masana'antu ta Najeriya wato TUC (Trade Union Congress), ta buga ƙararrawa dangane da yadda adadin jihohi dake rike da basussukan albashin ma'aikata suke hauhawa da a yanzu sun kai 35 in banda jiha daya.

Shugaban kungiyar Bobboi Bala Kaigama, shine ya shaidawa manema labarai wannan batu a bayan fagen taron jiga-jigan kungiyar na kasa da aka gudanar a jihar Legas, inda yace jihar Legas ita kadai ce ta sakarwa ma'aikata marar su.

Shugaban kungiyar Masana'antu - Bobboi Bala Kaigama

Shugaban kungiyar Masana'antu - Bobboi Bala Kaigama

Kungiyar ta gargadi gwamnatin jihohi da suke karkatar da akalar kudaden da aka tanada domin biyan albashin ma'iakata wajen wasu bukatun su na daban.

KARANTA KUMA: INEC ta fitar da jadawalin gudanar da zabe na shekaru 36 masu gabatowa

Kaigama yake cewa, in banda jihar Legas, babu wata jiha da bata rike makogoron ma'aikatan ta ba ko dan yaya baya ga malalo ma su kudaden Paris Club da gwamnatin tarayya a lokuta daban-daban.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Majalisar Dinkin Duniya ta fusata kwarai da aniyya kan 'Yan Matan Dapchi da 'yan ta'addan Boko Haram suka yiwa dibar Karen Mahaukaciya kimanin makonnin biyu da suka shude.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel