Nigerian news All categories All tags
Operation Cat Race: Sojoji sun gargadi jama’a

Operation Cat Race: Sojoji sun gargadi jama’a

- Rundunar sojin Najeriya ta samo wasu makamai a aiki da take gudanarwa na Operation Cat Race

- Ta gargadi mutane da su hankalta da makiyaya da ke neman mafaka

- Ta yi bayanin cewa babu mamaki jami’an tsaro suke gujemawa

Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da kokarinta na ganin ta wanzar da zaman lafiya kan rikicin makiyaya da manoma ta hanyar gudanar da gagarumin bincike a Adamawa wanda ya kai ga samo makamai da yawa.

A wata sanarwa daga Birgediya Janar Texas Chukwu wanda ya kasance kakakin rundunar, an gudanar da aikin ne a ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu.

Operation Cat Race: Sojoji sun gargadi jama’a

Operation Cat Race: Sojoji sun gargadi jama’a

An samo wasu bindigogi, mashi da kuma kibiyoyi a lokacin Operation Cat Race.

KU KARANTA KUMA: Kudurin kirkirar Peace Corps: Majalisar wakilai ta yi alla-wadai da kin amincewar Buhari

Rundunar ta gargadi mutane da su hankalta da makiyaya da ke neman mafaka a wajensu, cewa babu mamaki jami’an tsaro suke gujemawa.

A halin dake ciki majalisar dinkin Duniya ta bayyana fushin ta dangane da sace 'yan mata 110 na makarantar garin Dapchi a jihar Yobe, sakamakon harin 'yan ta'adda na Boko Haram kwanaki goma da suka gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel