Nigerian news All categories All tags
Kotu ta bar tsohon shugaban NNPC mai maqudan daloli damar yaje asibiti a kasar waje

Kotu ta bar tsohon shugaban NNPC mai maqudan daloli damar yaje asibiti a kasar waje

- An dade ana shari'ar su Andrew Yakubu da dalolinsa

- An kama shi da dala kusan miliyan goma a gida

- Andrew Yakubu ya shugabanci NNPC

Kotu ta bar tsohoon shugaban NNPC mai maqudan daloli damar yaje asibiti a kasar waje

Kotu ta bar tsohoon shugaban NNPC mai maqudan daloli damar yaje asibiti a kasar waje

Wata kotu a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja ta baiwa tsohon shugaban NNPC Andrew Yakubu damar yaje asibiti a kasar waje don ya duba lafiyarsa, kafin ya dawo a ci gaba da yi masa sharia kan Naira biliyan ukku da ya shirge a gida cikin daloli.

A Kaduna ne a bara aka kama kudaden, inda ya boye su cikin sef-seff a shirye a wani tsohon gida a sabon tasha a cikin unguwar talakawa.

A cikin shekaru na 2012 zuwa 2014 ne dai ya ce ya tara kudaden, dala miliyan har goma da yace kyauta ce aka bashi.

DUBA WANNAN: APC tace Buhari ne dan takarar ta a 2019

Kudaden dai har yanzu suna kulle a asusun babban banki CBN, shi kuma EFCC na kan bincikar yadda ya sami kudin.

An tafka sata a gwamnatin PDP ta Goodluck Jonathan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel