Nigerian news All categories All tags
Tsohon mataimakin gwamnan CBN na neman takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin gwamnan CBN na neman takarar shugaban kasa

- Yayi aiki a CBN da majalisar dinkin duniya a babbar kujera

- Ya ce saboda faduwar gwamnatoci a mulki ne ya ga dole ya fito takara

- An fara shirin shiga zabukan firamare a cikin gida

Tsohon mataimakin gwamnan CBN na neman takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin gwamnan CBN na neman takarar shugaban kasa

Tsohon jami'in majalisar dinkin duniya kuma tsohon mataimakin gwamnan babban bankin kasa CBN Kingsley Moghalu, ya ayyana bukatarsa da niyyar takarar shugabancin kasar nan a zabuka masu zuwa a 2019.

A cewarsa, saboda kasawar shuwagabannin kasar nan a lokuta da dama, yasa dole ya nemi takarar shugabancin domin samar da sabon tsarin shugabanci da ma sama wa kasar nan alkibla mai dorewa.

DUBA WANNAN: Mun sha da kyar daga hannun Boko Haram, matan Dapchi

A lokuta da dama, ana samun masu son yin takara a matsayin shugabanni, amma ko a cikin jam'iyyunsu basu iya taka wata rawa ta kuzo ku gani.

Siyasar Najeriya sai mutum yana da uban gida, ko kudi mai tarin yawa, ko kuma talakawa maasu yawa da soyayya. Ga alama irinsu Kingsley sai dai su nemi suna kawai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel