Nigerian news All categories All tags
Majasilar dattijai ta bayyana wadanda ke jawo cikas a zartar da kasafin kudin shekarar nan

Majasilar dattijai ta bayyana wadanda ke jawo cikas a zartar da kasafin kudin shekarar nan

- Majalisar wakilai ta bayyana cewar ba ta da hannu a jinkirin da ake samu wajen zartar da kasafin kudin shekarar nan

- Ta dora laifin a kan ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya

- Mataimakin shugaban kwamitin kasafin kudin majalisar, Sonny Ogbuoji (dan jam'iyyar PDP daga jihar Ebonyi) ya sanar da hakan

Majalisar dattijai ta wanke kanta daga zargin kawo cikas a zartar da kasafin kudin shekarar nan da shugaba Buhari ya mika gaban ta tun karshen shekarar da ta gabata.

Majalisar ta dora laifin jinkirin zartar da kasafin a kan shugabannin ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da su ka gaza mikawa majalisar cikakken rahoto a kan kasafin ma'aikatun da su ke jagoranta kamar yadda majalisar ta bukata. Kazalika majalisar ta yi kurarin daukan mataki a kan shugabannin hukumomin da ma'aikatun da basu mika bayanan ga kwamitin kasafin ba.

Majasilar dattijai ta bayyana wadanda ke jawo cikas a zartar da kasafin kudin shekarar nan

Shugaba Buhari yayin gabatar da kasafin kudi gaban majalisa

Mataimakin shugaban kwamitin kasafin kudi a majalisar, Sonny Ogbuoji (dan jam'iyyar PDP daga jihar Ebonyi) ya bayyana hakan yayin da yake bayyanawa manema labarai matsayin kasafin shekarar nan.

Ogbuoji ya ce duk da karin wa'adin sati guda a kan kokarin da majalisar ta bayyana zata rufe karbar kasafin ma'aikatun da hukumomin, har yanzu 63 daga cikin su basu mika takardun su ba.

KARANTA WANNAN: Satar Daliban Dapchi: Hukumar sojin saman Najeriya ta karyata rahoton baza jiragen yaki 100

Kazalika ya bayyana cewar wasu ma'aikatu da hukumomi da aka umarci su je su yi gyara a kasafin ma'aikatun su har yanzu basu kara dawowa ba.

Sanatan ya ce duk da haka yanzu sun kara bayar da wa'adin sati guda ga ma'aikatun kuma bayan karewar wa'adin ba zasu jira kowa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel