Nigerian news All categories All tags
Majalisar dinkin Duniya ta fusata akan 'Yan Matan Dapchi, za ta tallafawa Najeriya

Majalisar dinkin Duniya ta fusata akan 'Yan Matan Dapchi, za ta tallafawa Najeriya

Majalisar dinkin Duniya ta bayyana fushin ta dangane da sace 'yan mata 110 na makarantar garin Dapchi a jihar Yobe, sakamakon harin 'yan ta'adda na Boko Haram kwanaki goma da suka gabata.

Mista Antonio Guterres, babban sakataren majalisar da sanadin mai magana da yawunsa, Mista Stephane Dujarric, yayi tir tare da Allah wadai dangane da wannan hari da ya afku na dauke 'yan mata sama da dari.

Guterres yayi matukar fusata tare ta bayyana damuwar sa ta kololuwa dangane da dauke daliban mata a harin da ya afku na makarantar Dapchi ta jihar Yobe a ranar 19 ga watan Fabrairu.

Majalisar dinkin Duniya ta fusata akan 'Yan Matan Dapchi

Majalisar dinkin Duniya ta fusata akan 'Yan Matan Dapchi

Babban Sakataren yayi nemi a sako dukkanin 'yan matan cikin gaggawa ba tare da samun rauni ko kadan na lafiyar su domin kwanciyar hankalin iyayen su.

KARANTA KUMA: Dalibai 5 na makarantar Dapchi da suka tsallake fadawa hannun 'yan Boko Haram, sun bayar da labari mai sanya hawaye

Shugaban majalisar ya kirayi hukumomin tsaro na Najeriya akan su tsaya tsayin daka wajen tabbatar da ceto wannan 'yan mata tare da tabbatar da fushin shari'a kan masu hannu cikin wannan aika-aika.

Guterres ya kuma bayyana alwashi tare goyon baya na tallafawa gwamnatin Najeriya da wasu kasashen da abin ya shafa wajen yakar duk wani nau'i na ta'addanci a yankunan su.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, dalibai biyar na makarantar Dapchi da suka tsallake rijiya da baya a yayin wannan hari sun bayar da labari mai ratsa bargo da kashin duk wani mai tausayi a zuciya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel