Nigerian news All categories All tags
Satar Daliban Dapchi: Hukumar sojin saman Najeriya ta karyata rahoton baza jiragen yaki 100

Satar Daliban Dapchi: Hukumar sojin saman Najeriya ta karyata rahoton baza jiragen yaki 100

Hukumar sojin saman Najeriya ta karyata rahoton dake yawo a gari cewar ta baza jiragen yaki 100 domin neman 'yan matan Dapchi 110 da aka sace.

Hukumar sojin saman ta bayyana cewar rahoton da ake alakantawa da mai bawa shugaban kasa shawara a harkar tsaro ba gaskiya bane.

Hukumar sojin saman ta ce "tabbas mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Mohammed Monguno, yayin ziyarar da ya kaiwa gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, ya ambaci adadin atisayen da jiragen saman rundunar mu su ka yi cikin kankanin lokaci bayan bacewar 'yan matan. Hakan ko kadan ba yana nufin adadin jiragen da muka baza sararin samaniya ba kenan."

Satar Daliban Dapchi: Hukumar sojin saman Najeriya ta karyata rahoton baza jiragen yaki 100

Jiragen hukumar sojin Najeriya

A wani labari mai kama da wannan, shugaban rundunar sojin sama ta kasa, Abubakar Sadique, ya koma sansanin sojin sama dake Maiduguri domin kara ninka sintirin dakarun soji domin ceto 'yan matan na Dapchi.

KARANTA WANNAN: Fasto ya yi kyautar gidan mai, kamfani da alkawarin sayan jirgi ga matar sa a bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ta

Mai bawa shugaban kasa shawara a bangaren tsaro da shugaban rundunar sojin sama sun ziyarci gwamnan jihar Yobe, inda su ka yi wata tattaunawa mai muhimmanci dangane da satar 'yan matan.

Tun bayan satar 'yan matan ranar litinin, 19 ga wata, hukumar sojin sama ke shawagi a sararin samaniyar jihar Yobe domin gano inda mayakan kungiyar Boko Haram su ka boye 'yan matan.

Jiragen da hukumar ke amfani da su sun hada da wasu jiragen yaki na zamani masu daukan hoto daga sama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel