Nigerian news All categories All tags
Zazzaɓin Lassa ya ci gaba da addabar al'ummar Najeriya

Zazzaɓin Lassa ya ci gaba da addabar al'ummar Najeriya

Annobar Zazzaɓin Lassa ta ci gaba da yaduwa tare da addabar al'ummar Najeriya, yayin da aka samu wasu sabbin mutane 54 dauke da kwayoyin cutar a jihohi takwas na kasar na kamar yadda kididdigar bincike na cibiyar lafiya ta Najeriya ta tabbatar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a tsakanin 1 ga watan Janairu zuwa 25 ga watan Fabrairu na shekarar 2018, an samu mutane 1,081 dauke da kwayoyin cutar ta Lassa cikin jihohi 18 na Najeriya wanda a yanzu rayuka 90 sun salwanta.

Cikin makonni shidda na farko a shekarar 2018, an samu mutane 458 dauke da kwayoyin cutar, wanda binciken kwararru na kiwon lafiya suka tabbatar da ita a jikin mutane 125, da a yanzu 36 sun ce ga garin ku nan cikin jihohi 27 dake fadin kasar nan.

Zazzaɓin Lassa

Zazzaɓin Lassa

Rahotanni sun bayyana cewa, kaso 69 cikin 100 na wadanda suke kamu da cutar a sabuwar shekarar nan sun fito ne daga jihohin Edo da kuma Ondo, inda sabon bincike na kwana-kwanan nan ya tabbatar da cewa, an samu wasu mutanen daga jihohin Nasarawa, Ebonyi, Filato, Imo, Kogi da kuma jihar Ekiti da suke hadar har da ma'aikatan kiwon lafiya 14 a kasar nan.

KARANTA KUMA: Mashawartan shugaba Buhari na kawo koma baya a Najeriya

Legit.ng ta fahimci cewa, a makon da ya gabata ne a kwantar da mutane 42 a babban asibitin Irrua na jihar Oyo, inda mutane goma da suka riga mu gidan gaskiya a kwana-kwanan nan sakamakon cutar suka fito daga jihohin Ondo, Edo, Filato, Ekiti da kuma Ebonyi.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, dalibai biyar na makarantar Dapchi da suka tsallake afkawa hannun 'yan ta'adda sun bayar da wani labari mai ratsa bargo da kashin duk wani ma'abocin tausayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel