Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari ya sake nada wanda Jonathan ya tura hukumar NEPC

Shugaba Buhari ya sake nada wanda Jonathan ya tura hukumar NEPC

- Ana sa rai tazarcen Olusegun zata kara habaka harkar ffidda kayayyakin kasar nan zuwa kasashen waje

- Shugaba Jonathan ne ya fara kawo Awolowon hukumar

- Ga alama yayi babban kokari da hobbasa a hukumar, abu da ya sanya Buhari ya ci gaba da aiki dashi

Shugaba Buhari ya sake nada wanda Jonathan ya tura hukumar NEPC

Shugaba Buhari ya sake nada wanda Jonathan ya tura hukumar NEPC

Olusegun Awolowo a karo na biyu, a matsayin Executive Director/Chief Executive Officer na hukumar Nigerian Export Promotion Council, watau NEPC.

Bayanan na fitowa ne daga ofishin Femi Adesina, kakakakin shugaban Muhammadu Buhari, a shafinsa na facebook ta yanar gizo a ranar Laraba.

Takardar kuma na dauke da sa hannun Boss Mustafa, sabon sakatarn mulki na gwamnatin ta Buhari.

DUBA WANNAN: Kwastam ta kama motoci 777 a jihar Legas

Ita dai hukumar ta NEPC ita ke kula da duk wata hada-hada ta fitar da kaya da ake yi a kasar nan, wanda hakan ke kawo wa kasar nan kudaden shiga da ma habaka tattalin arziki, musamman yanzu da ake kokari kan harkar noman sayarwa kasashen waje.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel