Majalissar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da sace dalibai 110 da Boko Haram suka yi a jihar Yobe

Majalissar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da sace dalibai 110 da Boko Haram suka yi a jihar Yobe

- Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwar sa akan 'yan matan GSS Dapchi da Boko Haram suka kara sacewa a jihar Yobe

- Antonio Guterres yayi kira da gwamnatin Najeriya ta gaggauta kubutar da 'yan matan da Boko Haram suka sace

Majalissar Dinkin Duniya (UN) ta nuna damuwarta akan sace dalibai mata 110 na makarantar sakandare ta Dapchi da ke jihar Yobe.

Sakataren majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana haka a cikin wani jawabi da mi magana da yawun bakin sa, Stephane Dujarric ta fitar, inda ya yi Allah wadai da wannan al’amari da sakacin da ya janyo haka.

Majalissar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da sace dalibai 110 da Boko Haram suka yi a jihar Yobe

Majalissar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da sace dalibai 110 da Boko Haram suka yi a jihar Yobe

Ya ce hankalin sa ya tashi sosai a lokacin da ya samu labarin yadda aka kutsa cikin makaranta aka sace daliban mata har guda 110.

KU KARANTA : Kwastam ta kwace motoci 177 iyakar Legas

Antonio Gutteres ya ja kunnen gwamnatin Najeriya ta gaggauta kubutar da daliban tare da kamo maharan da suka sace su.

Daga karshe ya kara jaddada goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya UN ga gwamnatin Najeriya akan kawo karshen ‘yan ta’adan Boko Haram a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel