Nigerian news All categories All tags
Saraki yayi kira ga 'yan majalissar jihohi da su zartar da dokar hana biyan tsofaffin gwamnoni kudaden fansho

Saraki yayi kira ga 'yan majalissar jihohi da su zartar da dokar hana biyan tsofaffin gwamnoni kudaden fansho

- Majalissar Dokoki na jihar Kwara ta zartar dakatar da doka hana biyar tsofaffin gwamnoni kudin fansho

- Saraki yaba wa 'yan majalisar dokokin jihar Kwara akan dakatar da biyar tsofaffin gwamnoni kudaden fansho

Shugaban majalissar Dattawa, Dakta Bukola Saraki, yayi kira ga majalissar dokoki jihohin Najeriya da su bi sahun majalissar jihar Kwara wajen zartar da dokar hana biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakan su kudaden fansho

A ranar Talata majalissar Dokoki na jihar Kwara ta zartar da hukuncin dakatar da biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakan su kudaden fansho

.A ranar Laraba, Dakta Bukola Saraki ya fito, ya yaba wa kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Ali Ahmad, akan zartar da hukuncin.

Saraki yayi kira ga 'yan majalissar jihohi da su dakatar da dokar biyan tsofaffin gwamnoni kudaden fansho

Saraki yayi kira ga 'yan majalissar jihohi da su dakatar da dokar biyan tsofaffin gwamnoni kudaden fansho

Saraki yace yana cikin mutanen da suka ingiza majalissar dokokin jihar Kwara ta zartar da dokar.

KU KARANTA : Shugaba Buhari ya baiwa jahohin Najeriya bashin Naira 1.9 tiriliyan daga asusun rarar man fetur

Dakata Bokula Saraki, yayi gwamnan jihar Kwara daga shekara 2003 zuwa shekara 2011.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel