Nigerian news All categories All tags
PDP ce silar kara wa'adin shugabannin jam'iyyar APC

PDP ce silar kara wa'adin shugabannin jam'iyyar APC

- Zangon shugabannin jam'iyyar APC zai kare ne ranar 30 ga watan Yuni

- Jam'iyyar PDP ta zuba idanu don ganin yadda zata kare idan jam'iyyar APC ta yi zaben sabbin shugabanni

- A taron masu ruwa da tsaki da jam'iyyar APC ta gudanar, ta amince da dukkan shugabannin jam'iyyar su cigaba a matsayin shugabannin rikon kwarya

Wa'adin mulkin shugabannin jam'iyyar APC na kasa zai kare ne ranar 30 ga watan Yuni na shekarar nan.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewar ta saka idanu don ganin yadda zata kare bayan jam'iyyar APC ta gudanar da zaben sabbin shugabanni. PDP ta ce zaben sabbin shugabanni zai farraka kan magoya bayan jam'iyyar.

PDP ce silar kara wa'adin shugabannin jam'iyyar APC

PDP ce silar kara wa'adin shugabannin jam'iyyar APC
Source: Twitter

Duk da kasancewar Bola Ahmed Tinubu, jigo a jam'iyyar APC ya shawarci shugaba Buhari a kan a gudanar da zaben sabbin shugabanni, jam'iyyar ta jinjina irin fitinar da kan iya biyo bayan zaben ya saka ta jingine batun gefe guda.

KU KARANTA: Sabon salo: Yadda iyaye mata a Ghana ke yiwa yara bilicin tun su na ciki

A yanzu haka jam'iyyar APC ta bakin kakakin ta, Bolaji Abdullahi, ta bayyana cewar ta yanke shawarar kara wa'adin shugabannin jam'iyyar har na shekara guda bayan karewar zangon su a watan Yuni.

Jam'iyyar ta yanke wannan shawara a taron da ta gudanar na masu ruwa da tsaki karo na biyar da ta gudanar jiya a Abuja. Hakan na nufin jam'iyyar ba zata samu sabbin shugabanni ba sai bayan zaben 2019.

Jam'iyyar APC ta yi hakan ne bayan nazarin abinda ya biyo baya na rabuwar kayuwa a jam'iyyar PDP bayan ta gudanar da zaben sabbin shugabanni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel