Kwastam sun kama motoci 18 da buhunan shinkafa sama da 4000 a watan Fabrairu

Kwastam sun kama motoci 18 da buhunan shinkafa sama da 4000 a watan Fabrairu

- Jami'an hukumar kwastam reshen jihar Legas sunyi nasarar kama ababe da dama cikin watan Fabrairun 2018

- Kwantrollan yankin, Mohammed Uba ne ya bayyana ababen da hukumar suka gama yayin da yake jawabi a ranar Laraba

- Kayayakin da aka kama sun hada da motocin alfarma guda 18, buhunan shinkafa 4,201 da ma sauran kayayakin abinci da na masarufi

Jami'an Hukumar Yaki da masu fasakwabri wanda a kafi sani Kwastam da ke yankin Ikeja sun bayyana cewa rundunar ta kama motoci guda 18 da kudin su ya kai naira miliyan 303 wanda a kayi yunkurin shigo da su ta haramtaciyyar hanya cikin watan Febrairun 2018.

Jami'an hukumar Kwastam sun kama buhunan shinkafa 4,000 da motoci 18 a watan Fabrairu

Jami'an hukumar Kwastam sun kama buhunan shinkafa 4,000 da motoci 18 a watan Fabrairu

A yayin da yake jawabi ga manema ranar Laraba, Kwantrollan rundunar, Mohammed Uba ya ce an shigo da motocin ne ta tituna wanda hakan ya sabawa dokar da gwamnatin Najeriya ta kafa.

DUBA WANNAN: Dalilan da ya sa Buhari ya ki rattaba hannu kan kudirin kafa 'Peace Corps'

An kama motocin ne a hanyar Ijebu Ode da ke jihar Ogun kuma tuni an kulle su a dakin ajiye kaya na hukumar ta kwastam.

Sauran abubuwar da hukumar ta kama cikin wantan Fabrairun sun hada da buhunan shinkafa masu nauyin kilogram 50 guda 4,201 wanda kudin su ya kai naira miliyan 52, ganyen wiwi, sinkin tufafi na gwanjo, tayoyi mota na hannu, da yankakun kaji.

Sauran abubuwan sun hada da man gyda, na'urar kompressor da kuma kahon giwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel