Nigerian news All categories All tags
Dalibai 5 na makarantar Dapchi da suka tsallake fadawa hannun 'yan Boko Haram, sun bayar da labari mai sanya hawaye

Dalibai 5 na makarantar Dapchi da suka tsallake fadawa hannun 'yan Boko Haram, sun bayar da labari mai sanya hawaye

Dalibai biyar na makarantar sakandire ta mata dake garin Dapchi a jihar Yobe sun bayar da labari mai ratsa jiki, yayin da suka tsallake fadawa hannun 'yan ta'adda na Boko Haram a harin da suka yashe kimanin dalibai 110 a makon da ya gabata.

Wannan lamari dai ya jefa al'ummar garin Dapchi ciki razani da dimaucewa yayin da 'yan ta'addan suka kai hari wannan makaranta da ya sanya gwamnati ta rufe ta zuwa wani lokaci na gaba.

Sai dai an fara sa rai tare da fatan nasara a yankin yayin da wasu daliban suka tsere daga hannun 'yan ta'addan.

Daliban makarantar Dapchi

Daliban makarantar Dapchi

A wata ganawa ta musamman da manema labarai na Channels Television, daya daga cikin daliba da suka tsallake rijiya da baya, sun bayar da labari mai ratsa kashi da bargon duk wani mai tausayi.

Suke cewa, "babu shakka har yanzu suna cikin firgici tare da damuwa na dauke abokan su da suka hadar har da wadanda suka shakikan juna, kuma suna fatan gwamnati za ta ci ga da fadi tashin dawowa da daliban gidajen iyayen su."

KARANTA KUMA: Mashawartan shugaba Buhari na kawo koma baya a Najeriya

Legit.ng ta fahimci cewa, yau kwanaki goma kenan da sace daliban, yayin da iyaye da shugabannin makaranta ke mika kokon barar su ga gwamnatin jihar Yobe da kuma tarayya domin ganin an ceto 'yan matan daga hannun 'yan ta'addan.

A halin yanzu, shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin nuna halin damuwa, ya bayar da tabbaci ga 'yan Najeriya na ceto wannan dalibai daga hannun mamugunta.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wasu 'yan fashi da makami sun ce matsin tattalin arziki da sace-sacen jigan jigan gwamnati ya sanya suka sanya taguwar ta'addanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel