Lauya ya zargi wasu jami'an hukumar NDLEA da yi masa fashi da makami tare da yin garkuwa da shi

Lauya ya zargi wasu jami'an hukumar NDLEA da yi masa fashi da makami tare da yin garkuwa da shi

- Wani lauya ya zargi wasu jami'an hukumar NDLEA da yin garkauwa da shi tare da yi masa fashi

- Chinedu Nweke ya ce jami'an NDLEA sun tilasta shi ciro musu N160,000 a Banki

Wani lauya mazaunin jihar Legas mai suna, Chinedu Nweke, ya nemi a gurfanar da wasu jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi NLDEA reshen jihar Enugu da suka yi garkuwa dashi tare da yi msa fashi da makami.

Legit.ng ta samu rahoton cewa, wasu jami’an hukumar NDLEA sun tare lauya akan Independence Layout dake jihar Enugu a cikin wata farar Toyota Hilux da bindigogi suka tilasta shi shiga cikin motar su.

Ya ce daganan suka garzaya da zuwa shi wurin ATM din Bankin Diamond dake Ogui Road inda suka tursasa shi ciro musu N160,000.

An zargi wasui jami'an hukumar NDLEA da yiwa wani lauya fashi tare da yin garkuwa da shi

An zargi wasui jami'an hukumar NDLEA da yiwa wani lauya fashi tare da yin garkuwa da shi

Chinedu Nweke ya ce, yayi ihu a lokacin da yaga wasu 'yan sanda sun zo wucewa akan hanya, da suka ji ihun sa sai suka zo wurin dan ganin abun dake faruwa, amma da aka basu cin hanci sai suka wuce.

KU KARANTA : Rauni zai hana Neymar karawa da Ronaldo na Madrid

Lauyan ya ce, jami’an NLDEA sun sake shi ne bayan sun kwace N50,000 daga hannun wani direban taksi mai suna Amaechi.

Chiedu Nweke ya shigar da karar hukumar NDLEA reshen jihar Enugu a kotu akan yin garkuwa da shi tare da yi masa fasi da jami’an sa suka yi mishi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel